18 Nuwamba 2021 - 11:33
​Wani Bafalasdine Ya Rasu Saboda Rashin Kula A Gidan Kason Yahudawan Sahyoniyya

Wani bafaladine ya rasa ransa a cikin kurkukun da ake tsare da shi a cikin yankunan falasdianwa da aka mamaye saboda rashin kula daga hukumomin gidajen yarin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto cibiyar cibiyar yada labarai na falasdinawa tana fadar haka a safiyar yau Alhamis ta kuma kara da cewa sunan bafalasdinen shi ne Sami Al-Amour ba tare da yin wani karin bayani ba.

A halin yanzu ma akwai Palasdinwa 5 da suke yajin cin abinci don nuna rashin amincewarsu da tsarewar da gwamnatin HKI take masu ba tare da bayyana dalilin yan haka ba.

Khalid Fasfous danuwan daya daga cikin masu yajin aikin ya fadawa tashar talabjin ta Al-alam kan cewa dan’uwanda yana iya rasuwa a ko yauce don ya dauki kwanaki 125 bai ci abinci ba, kuma har ya kasa magana.

342/